Kalaman Soyayya Zuwa Ga Masoya

Kalaman Soyayya Zuwa Ga Masoya

DOWNLOAD NOW

Kalaman Soyayya Masu Dadi Da Nishadi
Barka da kasancewa cikin wannan rana masoyiyata. Dukanin rayuwata na karanta, nayi Mafarkinta, na jirata, nayi kuka don ita,

yanzu haka na gano kece kadai abar kaunata. Tun farkon haduwata dake zuciya ta aminta dake a matsayin mai debe mata kewa. Soyayyar da na ke yi miki tamkar tafiyace mai nisa da na fara yinta wadda bata da lokacin yankewa har abada.

Nasan burina zai cika matukar ina tare da ke domin kuwa dukkanin burina yanzu bai wuce samun ki a matsayin matata uwar ‘ya’yana. Ina son ki fiye da zinariya.


Kyakykyawar zuciyar kice ta bayyana kyawawan halayyar ki, wadanda suke sakamin cikakkiyar nutsuwa a cikin ruhina Sama cike take da taurari masu hasken da ke haske duniya a cikin kowanne dare.

Amma haske mafi haskaka fuska da yaye duhun zuciya, na gan shi ne a cikin idanuwanki. Ki Kula Min Da Kanki. Ina Son ki. kasantuwar mu a raye cikin ruhi guda d’aya ya sanya zuciyoyin mu bugawa cikin lokuta makamanta juna.


Furanni na furta kalmomin yabo a kanki a dukkan lokacin da na shiga lambu mai d’auke da ‘korama gami da korayen ciyayi da bishiyoyi masu d’auke da tsintsaye.

Sukan rera baitukan yabo a gare ki, cikin harshen da zuciya ce kawai ke iya fahimtarsa. Ina Son Ki. Masoyi k`aine wanda zuciya ta ta aminta da shi.


Ina son ka kara sani cewa babu wani da namiji wanda zuciyata ta gama aminta da dukkan soyayyar sa face kai.

Ina Son Ki, ba da Zuciyata ba kuma ba da tunanina ba. Zuciya za ta daina aiki, tunani zai mance. Ina Son Ki da Ruhina ne, saboda Ruhi bai daina aiki, kuma ba ya mantuwa.
FAST DOWNLOAD


How To Download Movies On ArewaLimited