Hadin Maganin Karfin Maza Da Namijin Goro, Maganin Karin Ni'ima A Gaban Mace
A yau zamuyi bayanin hanyar da za'a bi domin samun karfin mazakuta cikin sauki ba tare da kashe kudi ba,kuma wannan hanya bata da illa ga lafiya,sai dai kara lafiya.
HADIN KARFIN MAZA
Ka samu: Garin Namijin Goro Da Zuma
Da farko za'a samu Zuma tacecciya mai kyau a kwaba ta da garin Namijin goro idan baka samu ba ka siya ka shanya ya bushe ka dake shi, sai a rika shan chokali 3 sau 2 a rana,zakai mamaki sosai.
Abin sadaqa ayiwa Annabi sallallahu Alaihi wasallam Salati.
FA'IDODIN TAFARNUWA (Garlic)
Ita dai tafarnuwa wata babbar kyauta ce daga allah dayabamu mu mutane yan Adam wasu mutanen in akace tafarnuwa suna dauka maganin sanyi kadai takeyi amma bahaka abun yakeba
GA KADAN DAGA CIKIN AMFANINTA
Tafarnuwa tana maganin SANYI. Na danshi kona ko sanyin gari wanda yake haddasa mura kaikayin jiki kurajen damuna ciwon hakora ciwon kai da sauransu, hakanan ma yin turare da tafarnuwa yana maganin mayu kuma yana korar mugayen kwari kamar maciji kunama da makamantansa
Tafarnuwa ba anan tatsaya ba
Idan mace mai shayarwa tana so tasamu wadatar ruwan nono tare da ingantacciyar lafiya ga nonon sai tasamu dabino kamar guda 10 da habbatussauda cokali daya sai garin tafarnuwa Rabin cokali ahada adafa da ruwa kofi2 ta sha sau2 arana.
TAFARNUWA TANA MAGANIN CIWON CIKI DA CIWON MARA
Wanda mata suke samu Bayan haihuwa, sai a sami ruwa mai dumi kofi daya a zuba man tafarnuwa cikin cokalin shayi daya sai ta sha
ta yi haka kwana uku Wanda ke yin ba haya da kyar ko fitsari da kyar ko wajen fitar jinin haila sai an sha wuya ko jinin biki, sai ta rika shan karamanin cokali daya da safe daya da rana daya da dare, zata warke sai dai budurwar da take da budurcinta Idan ta fiya yawan yin amfani da man tafarnuwa zata rasa budurcinta.
TAFARNUWA TANA KARA NI'IMA GA MATA
Idan mace tana son ni'imar ta ya yawaita sai ta sami madarar saniya ko nonon rakumi kofi daya ta zuba man tafarnuwa ta sha kofi daya da safe, kofi daya da dare, matar da tayi haka zata bai wa mijinta sha’awa da mamaki matuka.
YADDA AKE AMFANI DA TAFARNUWA DOMIN TSUKE GABAN MACE YAKOMA DAN KARAMI
Daidai yadda zata gamsar da mijinta Sai ta sami "Turaren Misk Algazali" Rabin cokali ahada da cikin cokali daya na man tafarnuwa ta gauraya, sannan sai ta tsoma auduga mai kyau tasa a gabanta, bayan awa 3 sai ta cire ta yar da audugar tayi haka sau hudu ko sau biyar idan tayi haka gabanta zai dawo daidai
MAN TAFARNUWA YANA MAGANIN KAIKAYI MATSEMATSI
Idan namiji ko mace yana jin kaikayi a matse matsinsa to, sai ya sami garin jar kanwa cikin babban cokali daya, ya dafa da ruwa kofi biyu, idan ya tafasa sai ya zuba man tafarnuwa babban cokali biyu ya gauraya sannan ya sauke, idan ya huce sai ya wanke gabansa gaba daya da ruwan zai sami sauki.
INA WANDA BAYA IYA SADUWA DA IYALI
Wanda baya iya saduwa da iyali fiye da sau daya ko kuma da ya soma sai ya ji ya gaji, to sai ya sami dabino mai kyau ya dafa da ruwa mai kyau, idan ya tafasa sai ya tace zai dafa da ruwa kamar kofi hudu 3 bayan ya tace sai ya debi kofi uku ya sake tafasawa yana cikin tafasa sai ya zuba man tafarnuwa babban cokali biyu 2 sai ya barshi akan wutar ta yadda ruwan zai dawo kamar kofi biyu 2 idan ruwan ya huce sai ya rika sha babban cokai biyu sau hudu a rana, ya yi kwana 7 yana yin haka…
ALHAMDU LILLAH, A DAURE A JARRABA