Idan har kina neman maganin da zakiyi don gyaran nono ya daina zubewa kuma su tsaya chak, ta cika bulbul to ga hadin da zakiyi musamman ga budurwa, shi wannan hadi kuma kowace macema zata iya amfani dashi,
Ga yanda akeyi shine za a samu.
Zaki samu
1- Garin waken soya
2- Garin alkama
3- Garin zogale
4- Garin bawon lemun zaki
5- Kunfan maliya
6- Zuma
Sai ha dasu guri daya ki rinka shafawa a nonon bayan minti-30 ko sama da haka sai ki wanke, sannan kuma ki rinka shan kunun alkama zaki sha mamaki
Don Dawo Da Martabar Nono Da Girmansa
Ga matar da take son ta dawo da martabar nononta ko girmansa ga hadin da zatayi shine zata samu
Ganyen sabara mai kyau
Da 'ya'yan alkama suma masu kyau
Sai ki rinka nunu dasu, ko kunun gyada, ko kunun alkama, ko kunun shinkafa, ko kunun gero, ko ko ko duk dai wanda yasamu sai ki dafashi da wannan hadin mai albarka
Amarya Ga Tsaraba
Shi wannan hadin yana da banmamaki musamman wajen karin soyayya tsakaninki da mai gida, da martaba da farin cikin mai gida da nishadin amarya kuma yanasa maigida yaji dadin da bai misaltuwa zaki zama gagara gasar masu gasa,
Saboda shi wannan hadin manya mata ne
1- Ya'yan kankana
2- Danyar gyada mai kyau
3- Dabino
4- Alkama
5- Garin kumasoriyya
6- Ya'yan zogale
Sai ki dakesu suyi laushi ki rinka shan karamin cokali da madara ta ruwa safe da yamma kuma shima mijin zai iya sha.