Sabon Hadin Matsi Ga Mace Tare Da Yadda Gaban ‘Ya Mace Yake
Yanda Gaban Mace Yake:
mafi yawa daga cikin mutane basu san yanda gaban mace yake ba balle su
san cewa akwai wani waje da ake kira majiya dadi, kuma sanin hakan yana da muhimmanci domin duk macen da tayi sa’a mijinta yana tabo mata wannan wuri(majiya dadi) to zata ga son da yake mata yana karuwa dari bisa dari (100%) itama haka zata ji tana kara sonshi sosai
Ga Wani Hadin Don Matsewar Gaban Mace
wannan hadin ana yinshi shima don karin ni-ma da kuma matsawar gaban
mace,kuma yana sa hankalin mai gida yadawo kanki,sannan kuma yana sa
gaban mace kamshi sosai wannan hadin angwada amfani yana aiki sosai kayan da ake bukata sune:
1: Lemun tsami
2: Zuma mai kyau
3: Raihan
Yanda Ake Yi Shine:
zaki yayyanka wannan lemun tsamin saiki sakashi a ruwan dumi sai ki kawo raihan ki zuba, sai ki kawo zuma ki zuba sai ki rinka kama ruwa dashi tare da wanke duk wani lungu da
sako na gabanki ciki da waje,yin hakan yana sa mai gida ya rinka tabo maki
majiya dadi wannan wani bangare ne a cikin gaban mace.
A Wani Bangare Kuma Shin Ko Kisan Amfanin Kunun Fari ?
Ko kinsan tarin amfanin da Kanumfari ya keyi a jikin Mace? Yau ya kamata ki sani
Kamar yanda mata ke ajiye Zuma a gida haka yanzu mata basa rabuwa da kanunfari domin duk wani hadin daka na musamman ko hadin ruwan jaraba ko wani tsumi idan kuka bincika zakuga akwai sa hannun kanunfari don haka kema ki ajiye shi don burge mijinki.
Duk lokacinda zaki dafa shayi kada kimata dashi domin idan ya hadu da lefton yana aiki a jkin mace wajen karin ni’ima kuma ya na da kyau yajinki ya zama akwai kunfari aciki.
Ana Amfani da kanimfari wajen rage tumbi ki jika shi aruwa idan ya yini ajike sai kishanye ruwan ki kara wani zaki ga cikin ki ya saki kinyi bayan gida wannan shine alamar yayi miki aiki.
Ana Amfani da Kanimfari wajen maganin infection idan kika saka ruwa tafasashe a flast sai ki zuba shi aciki da ganyen magarya kirufe sai yayi kamar sa’a daya (1 hour) zaki yini kina yin tsarki dashi har zuwa dare.
Zaki iya daka garin kanimfari ki hadashi da totuwar raken dakika sha yabushe sai ki sami farin muski (miskul dahra) ki cakuda shi sosai da garin da totuwar raken da kuma muskin idan ya bushe sai ki ringa turaren tsugunawa dashi wannan kada ki barshi.
Muhimman Hanyoyin da ya kamata a bi don Karfafa Lafiya lokacin Sanyi.
Dazaran karshen shekara ya nufato, Sai a shiga yanayi na sanyi.
Hakan na iya zama kalubale ga lafiyar mutum ta hanya mafi saukin kamuwa da mura, tari, bushewan labba, da sauransu.
A kula da wadan nan shawarwari
1. A yawaita shan ruwa sosai
2. A yawaita wanke idanu akai akai domin gujewa kamuwa da ciwon ido.
3. A yawaita amfani da abin rufe fuska da hanci (Facemask)
4. A takaita zirga-zirga a waje sai dai wanda ya zama dole, mai mahimmanci.
5. A yawaita sa kaya masu dan kauri, ko rigunan sanyi domin sanya dumi a jiki.
6. A yawaita rufe tagogi da kofofin domin takaita shigowar kura daki.
7. A yawaita shafa mai a jiki domin dandashe fata kar ta bushe.
8. A yawaita shafa mai a labba domin kare su daga farfashewa ko tsagewa.