Shahararrin Mawaki Kuma Dan Fim Da Akafi Sani Da JJC Skillz Ya Karbi Musulunci

Shahararrin Mawaki Kuma Dan Fim Da Akafi Sani Da JJC Skillz Ya Karbi Musulunci


 

Mawaki kuma dan fim a Nollywood JJC Skillz wanda asalin sunan shi Abdurrasheed Bello ya ce dama shi asalin shi Muslunci ne kawai ya bi addinin mahaifiyarsa ce wacce ba Musulma ba Ya zanta da wata jarida, inda ya bayyana mata kadan daga dalilan da suka sa baiye addinin Islama abaya ba.

JJC Skillz ya bayyana dawowa addinin Islama, addinan da mahaifinsa ke kai. Jarumin na fina finan Nollywood kuma mijin jaruma Funke Akindele ya bayyana dawowarsa Islama ne a shafinsa dake Instagram.


Ya kuma tattaunawa da wata jaridar yanar gizo ta addinin Islama a ranar Alhamis don bayyana aniyarsa

JJC Skillz ya ce, dama an haife shi a matsayin Musulmi, kuma danginsa Muslmai ne masu suna sallah, amma ya bi addinin mahaifiyarsa wacce ba Musulma ba.

Allah ya ganar dani hanya 

A cewarsa: “Na kasance cikin bata amma yanzu na fahimta Ya Allah, ina rokon yafiyarka da lafiya a nan duniya da lahira. “Ya Allah, ya hijabance rauni na ka yaye mani bakin ciki, kuma ka kare ni ta baya da ta gaba na sannan ta dama na da hagu na da kuma sama na, kuma ina neman kariyarka kada na shagala da duniya."Post a Comment

0 Comments